(ABNA24.com) Janar Namata, zai maye gurbin Janar Hanena Ould Sidi, na Mauritania, wanda ke ja ragamar rundinar tun cikin watan Yuli na 2018.
Kafin a damka masa wannan mukamin, Janar Namata, shi ne mukadashin, babban hafsan sojin kasa na Nijar, kuma a bayyanasa a matsayin wanda ya taka gagarimar rawa wajen yaki da kungiyar Boko Haram.
Nadin na Janar Namata na zuwa ne gabanin wani taron gaggawa da da za’a gudanar a watan Satumba mai zuwa, a Ouagadugu, babban birnin kasar Burkina Faso, kan matsalar tsaro a kasashen 15 mambobin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS/CEDEAO.
Wasu majiyoyi daga gwamnatin kasar faransa, sun nakalto cewa, suna fatan sauyin da aka samu ya farfado da ayyukan rundinar, da suka suka fusknaci koma baya, a watannin baya bayan nan, wanda kuma tafiya a hakan ba zai sanya a samu tallafin kasa da kasa da ake bukata ba.
A shekara 2015 ne aka kafa rundinar kasashen na G5, Sahel, data hada da (Mauritania, Mali, Nijar, Burkina faso da kuam Chadi), da nufin yaki da ta’addanci da fataucin miyagun kwayoyi da mutane a yankin.
Saidai har kawo yanzu rundinar na fama da matsalar kudi domin tafiyar da aikinta gadan-gadan.
Kasashen duniya da dama dai sunyi wa kungiyar ta G5 Sahel alkawarin tallafi.
/129
25 Yuli 2019 - 06:59
Lambar labari: 964369
An nada Janar Umaru namata Gazama, na Nijar, a matsayin sabon kwamandan rundinar yaki da ta’addanci ta kungiyar G5 Sahel.